Galatians 6

Yin Alheri ga Kowa

1ʼYanʼuwa, in an kama wani a cikin zunubi, ku da kuke masu ruhaniya ya kamata ku komo da shi a kan hanya a hankali. Amma ka lura da kanka, in ba haka ba kai ma za ka jarabtu. 2Ku ɗauki nawayar juna, a haka kuwa za ku cika dokar Kiristi. 3In wani yana tsammani shi wani abu ne alhali kuwa shi ba kome ba, ruɗin kansa yake yi. 4Kowa yǎ auna ayyukansa. Saʼan nan ne zai iya yin taƙama da kansa, ba tare da kwatanta kansa da wani ba, 5gama kowa zai ɗauki kayansa.

6Duk wanda aka koya wa Maganar, yǎ ci moriyar abubuwansa na alheri tare da mai koyarwa.

7Kada a ruɗe ku: Ba a yi wa Allah baʼa. Mutum yakan girbe abin da ya shuka ne. 8Wanda ya yi shuki don yǎ gamshi mutuntakarsa, daga wannan mutuntaka zai girbi hallaka; wanda ya yi shuki domin yǎ gamshi Ruhu, daga Ruhu zai girbi rai madawwami. 9Kada mu gaji da yin nagarta, gama a daidai lokaci za mu girbe amfani in ba mu fid da zuciya ba. 10Saboda haka, yayinda muke da zarafi, bari mu aikata nagarta ga dukan mutane, musamman ga waɗanda suke na iyalin masu bi.

Ba Kaciya ba, Sai dai Sabuwar Halitta

11Ku dubi irin manyan-manyan harufan da na yi amfani da su yayinda nake rubuta muku da hannuna!

12Waɗanda suke son nuna bijinta a fili suna ƙoƙari su tilasta muku ku yi kaciya. Dalilin kaɗai da suke yin haka shi ne don gudun kada a tsananta musu saboda gicciyen Kiristi. 13Kai, su masu kaciya ma ba su kiyaye Doka ba, duk da haka suna so a yi muku kaciya don su yi taƙama kan an yi muku kaciya. 14Kada in taɓa yin taƙama ga kome sai dai a cikin gicciyen Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa aka gicciye duniya a gare ni, aka kuma gicciye ni ga duniya. 15Kaciya ko rashin kaciya ba sa nufin kome; abin da yake da amfani shi ne sabuwar halitta. 16Salama da jinƙai su tabbata ga dukan waɗanda suke bin wannan ƙaʼida, har ma ga Israʼila na Allah. 17A ƙarshe, kada kowa yǎ ƙara damuna, gama ina ɗauke tabbai masu nuna ni bawan Ubangiji Yesu. 18Alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi yǎ kasance tare da ruhunku, ʼyanʼuwa. Amin.

Copyright information for HauSRK